Jump to content

Ahmadu Atiku

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ahmadu Atiku
Sultan na Sokoto

Rayuwa
Haihuwa 1807
ƙasa Najeriya
Mutuwa 1866
Ƴan uwa
Yara
Sana'a
tambarin Ahmad atiku

Ahmadu Atiku (Haihuwa da Rasuwa:1807-1866) shi ne kuma aka fi sani da Ahmadu Zarruku Yayi Sultan na Sokoto daga shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari takwas da hamsin da tara 1859 zuwa shekarar ta alif dubu ɗaya da ɗari takwas da sittin da shida 1866. Kafin ya zama Sarkin Musulmi, ya kasance shugaban gidan Abu Bakr Atiku na gidan Uthman Ɗan Fodiyo kuma ya riƙe sarautar Sarkin Zamfara tare da ɗaukar nauyin garin Sakkwato da kudu maso gabashin Sakkwato. [1] Atiku ya kafa sansanin soja (ribat) a Chimmola wanda ke gefen kwarin daga garin Wurno kuma wanda yake amfani da shi wurin zama na gwamnati.

An kuma haifi Atiku a c. Shekarar 1807, aka zaɓe shi a matsayin Sultan a shekarar dubu ɗaya da ɗari Tara da hamsin da tara 1859 a bayan Ali Bello . Bello ya ci nasara sosai a yaƙi kuma ya kasance mai girmama mutane; a lokacin hawan Atiku mulki, Sokoto ta kafu sosai. [2] An zaɓe shi akan Ali ƙaramin, Sarkin Gobir, Isa da Umar Buhari, jika ga Uthman Ɗan Fodio . Atiku ya ci gaba da ƙoƙarin karfafa Ali Bello, ya kafa hakarkari ko matsugunan Moriki, Boko da Birnin Kaya a tsohuwar Zamfara da sasantawar Chafe, kudu maso gabashin Sakkwato. Raba, wani yanki da ke gefen Sakkwato ya fadada kuma a kudu, dan uwan Ahmad, Umaru Nagwamatse ya kirkiro masarautar Kontagora . [3] Atiku ya kuma karfafa matsugunan Sullubawa. Sullubawa gungiyoyin Fulfulde ne waɗanda suka riga suka zauna a ƙasar Hausa. Sullubawa sun fadada kauyukan Wamako, Dingyadi da Kilgori. Atiku ya gargadi Sullubawa da jama'a da su kiyaye doka kuma kada su karbi lada don dawo da dabbobin da suka bata, su daina sayar da gonaki, su yi biyayya ga kiran jihadi da sammacin Alkalis [4] Atiku ya kuma rage barazanar Gobirawa ta amfani da rarrabuwa tsakanin Sarkin Gobir Bawa na Gwanki da dafkaya daga cikin danginsa, yarima Dan Halima. Dan Halima ya kulla yarjejeniya da Atiku kuma aka bashi damar kafa sabon gari Sabon Birni yayin da aka karrama shi a matsayin shugaban duk Gobirawa a wannan sashin Masarautar. Garin ya zama abun kariya ga Sarkin Gobir Bawa.

  1. Last, M. (1967). The Sokoto Caliphate. New York: Humanities Press. p. 101
  2. Last. p.114
  3. Last. p.115
  4. Last. p. 117


Sarakunan Sokoto
Usman Dan Fodiyo | Muhammadu Bello | Abubakar Atiku | Ali Babba bin Bello | Ahmadu Atiku | Aliyu Karami | Ahmadu Rufai | Abubakar II Atiku na Raba | Mu'azu | Umaru bin Ali | Abderrahman dan Abi Bakar | Muhammadu Attahiru I | Muhammadu Attahiru II | Muhammadu dan Muhammadu | Hassan dan Mu'azu Ahmadu | Siddiq Abubakar III | Ibrahim Dasuki | Muhammadu Maccido | Sa'adu Abubakar